Kungiyar ActionAid tare da abokan hulɗarta — Partnership Against Violent Extremism Network (PAVE), da PCVE-KIRH — sun gudanar da taron kwanaki biyu a Kano domin tabbatar da binciken taswirar al’umma da aka gudanar kan batun tsattsauran ra’ayi a kananan hukumomi shida da al’ummomi goma sha biyu.

Taron, wanda ya ɗauki taken “Gina Haɗin Kai da Aiki Tare, da Tabbatar da Ingantattun Dabarun PCVE masu Dorewa”, ya zama dandali na tattaunawa tsakanin al’umma, jami’an tsaro, masu sarautun gargajiya, da ƙungiyoyin farar hula.
A yayin taron, jami’ar ActionAid da ke kula da shirin Kula da ke kula da bangaren yaki da tsattauran ra’ayi, Jamila Musa, ta bayyana cewa an gudanar da wannan bincike a kananan hukumomin Tudun Wada, Bebeji, Gwarzo, Bichi, Nasarawa da Karamar hukumar Gwale a Kano, da kuma al’ummomi goma sha biyu, domin gano ainihin abubuwan da ke haifar da tsattsauran ra’ayi da kuma hanyoyin magance su. Ta ce manufar taron ita ce tabbatar da sakamakon binciken tare da hada kan al’umma wajen bullo da shirin aiki mai dorewa.
A nasa jawabin, Wanda ya wakilci rundunar ‘yan sanda, DSP Hussaini Abdullahi, ya bayyana Kano a matsayin daya daga cikin jahohin da aka fi samun kwanciyar hankali a Najeriya, duk da kananan matsaloli irin su harkar daba da ake fuskanta. Ya jaddada cewa daba babban laifi ne da ke faruwa a cikin al’umma, kuma da hadin kan jama’a da bayanan sirri da suke samu, rundunar na daƙile wannan matsala yadda ya kamata.
Wasu daga cikin mahalarta taron, musamman jami’an tsaro da masu rike da sarautun gargajiya, sun yaba da sakamakon binciken da aka gabatar. Sun bayyana shi a matsayin wata hanya mai muhimmanci ta fahimtar matsalar daga tushe tare da shawo kan ta ta hanyar da ta dace. Sun kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin farar hula da al’umma wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da laifuffuka na hadari.
Taron ya kammala da kudirin samar da tsarin aiki wanda zai mayar da hankali kan inganta zaman lafiya, karfafa al’adu na fahimtar juna, da kuma bai wa matasa damar shiga ayyukan raya kasa domin rage yiwuwar fadawa cikin tsattsauran ra’ayi.