Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da aikin gina titin Kayarda–Tasha–Masakawa–Dan Alhaji da ke karamar hukumar Lere.

A cewar gwamnan, aikin na daga cikin shirin gwamnatinsa na inganta karkara, wanda zai bunƙasa tattalin arziki, rage gibin ci gaban da ke tsakanin birane da kauyuka, da kuma samar da sabbin ayyukan yi.
Lere dai na daga cikin manyan yankunan noma a Najeriya, musamman wajen samar da masara, tumatir, wake da rake.
“Haɗaɗɗiyar hanya a Lere za ta inganta rayuwar manoma, ta buɗe sabbin damarmaki na kasuwanci, da kuma tabbatar da dorewar arziki,” in ji gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da gaggauta aikin Pambegua–Saminaka–Jos Road, yayin da ake duba yiwuwar gyaran Saminaka–Kano Road saboda muhimmancinta ga harkokin kasuwanci da haɗin kai.
A nasa jawabin, Sarkin Lere, Alhaji Umar Suleiman, ya bayyana aikin a matsayin sauyi ga al’umma, inda ya ce titin zai ba da damar kai kayan gona kasuwa cikin sauƙi bayan shekaru na wahala.
Haka kuma, wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana farin cikinsu.
Ibrahim Zubairu, wani dattijo a Kayarda, ya ce sabon aikin zai rage asarar amfanin gona, yayin da wani ɗan ƙasa, Lawal Gambo, ya nuna farin ciki da matakin gwamnatin tarayya kan manyan hanyoyin da ke da muhimmanci ga zirga-zirgar al’umma.