Dakarun Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile yunkurin kai wani harin kwantan bauna da ’yan ta’adda suka yi ƙoƙarin kaiwa kan ayarin motocin sojoji masu rakiyar kayan agaji a yankin Kareto, karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya auku ne a ranar Laraba a kan hanyar Gubio–Damasak, inda ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka tada bama-bamai guda biyu kafin su bude wuta kan sojojin.
Wata majiya ta shaida cewa dakarun sun yi gaggawar ɗaukar shiri tare da budewa da wuta, lamarin da ya kashe ’yan ta’adda 13 nan take, yayin da sauran suka tsere. Sojojin sun bi sawunsu don kawar da sauran da suka tsere a yankin.
A yayin bincike, dakarun sun gano bindigogi AK-47 guda takwas, kwanson harsasai guda goma, da tarin harsasai na 7.62mm, da abubuwan fashewa, da kuma jerin bama-bamai da aka riga aka hada.
Soja daya ya samu rauni kaɗan, yayin da aka lalata tayoyi huɗu na motar MRAP, sannan motoci biyu suka kama da wuta yayin musayar wuta.
Majiyar ta kara da cewa nasarar da sojojin suka samu ta nuna ƙwarewa da juriyarsu, tare da tabbatar da cewa ƙoƙarin ’yan ta’addan na kawo cikas ga kai kayan agaji bai yi nasara ba.
Dakarun sun bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan kakkabe ‘yan ta’adda a yankuna domin hana su sake samun damar kai hare-hare, tare da tabbatar da hanyoyin samun agaji a yankin Arewa maso Gabas.