

Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana karara cewa ba zai yiwu ba a dogara ga baƙi ko ƙasashen waje wajen warware matsalolin tsaron da ke addabar Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, dole ne ‘yan ƙasa su fito su ɗauki alhakin dawo da cikakken zaman lafiya a faɗin ƙasar.Janar Musa ya bayyana wannan muhimmin matsayi ne a ranar Lahadi, yayin da yake jawabi a wurin taron “Cultural Night and Unity Ball” (Daren Al’adu da Taron Haɗin Kai), wanda Ƙungiyar Tsoffin Ɗalibai na Makarantun Haɗin Kai (USOSANS) ta shirya a Abuja.
Taron, wanda aka gudanar don tunawa da bambancin al’adu da ƙabilun Nijeriya, an yi shi ne domin ƙarfafa manufofin haɗin kan ƙasa da zaman lafiya a tsakanin tsoffin ɗaliban waɗannan makarantu.A jawabin nasa mai cike da kira ga kishin ƙasa, Janar Musa ya jaddada cewa: “Maganin matsalar tsaro a hannunmu take.
Dole ne kowane ɗan Nijeriya ya gane cewa alhakin ƙasar nan ya rataya a wuyansa, ba wai yan ƙasashen ketare ba.