
Yanzu-yanzu Ɗan wasan baya na Barcelona Alejandro Balde zai yi jinyar mako 3 zuwa 4.
Kungiyar Barcelona ta samu cikas bayan ɗan wasan baya, Alejandro Balde, ya samu rauni a yayin atisaye.
Rahoton gidan rediyon COPE ya bayyana cewa, Balde zai kasance a wajen fili na tsawon makonni uku zuwa hudu.
Wannan dai na zuwa ne bayan ƙungiyar tayi canjaras a wasan mako na uku a karshen makon da ya kamata.