
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, KanoAn bayyana Cigaban da ake samu ta fuskar Tsaron a yankin Sheka, Medile da Darmnawa da cewa ya samu ne sakamakon gagarumar gudunmawar rundunar ‘yan sanda da jami’an tsaronmu na sakai wadanda Suka hada da Vigilanti, Hunters, Mu hadu mu gyara, Scorpion da Civilian JTF.
Shugaban Kungiyar Muryar Jama’ar Sheka Servy. Malandi Umar Kura ne ya bayyana haka Alokacin da yake tattaunaws da kwanta tun tantance Jami’an tsaron sa Kai da ke Gudanar da aiki a wannan gari na Sheka Mai albarka.
Malandi Kura yace babu shakka hadin Kai, yin aiki tare da fahimtar juna ne babban dalilin samu wannan nasara musamman zaman lafiyar da aka samu cikin watanni biyu da suka gabata a Wannan yanki, wannan ce tasa muka kafa kwamitin da zai nazari tare da zakulo zakwakuran Jami’an mu na sakai wadanda ke aiki tukuri domin tattara Cikakken bayanansu, musamman idan akayi la’akari da barazanar shigowar wasu bata gari daga wasu makwbtan jihohin dake fama da matsalolin tsaro.
Ya Ci gaba cewa bayan gama aikin tantacewar ne kuma wannan Kungiyar ta muryar Jama’ar Sheka zata nemi hadin Kan hukumomin tsaro domin Bayar da horon sanin hanyoyin tsimakawa harkar tsaro domin hada karfin da karfe wajen tabbatar da dorewar zaman lafiyar Jihar Kano da Kasa baki daya.
“Ya zama wajibi Ga kowa ne mai kishin Jihar Kano ya jinjinawa kokarin Gwamnan Kano da rundunar ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaro na farin kaya da sauron hukumomin Tsaron Kan yadda suke aiki tukuru domin murkuahe duk wata barazanar tun bata je ko Ina ba, saboda haka Muryar Jama’ar Sheka taga dacewar yin wannan yunkuri domin taimakawa kokarin Gwamna da hukumomin tsaro Kan kokarin da suke na Tsaron rayuwa da dukiyoyin jama’a.
“A Karshe Servy Malandi ya jinjinawa kokarin Kwamitin lura da harkokin tsaro Kungiyar karkashin Alhaji Ibrahim Chidi bisa aikin da suke na tabbatar da nagartattun jami’an dake aiki tukuru wajen kare rayuka da duniyar Al’ummar Sheka da makwabtanta, wanda ya tabbatarwa Kwamitin yin aiki Kan shaqarwarin da zasu Bayar bayan gabatar da rahoton aikin nasu.