
Gudunmawar Alh. Sayyu Idris Damtata Ga Tsoffin Daliban WUCOBA CLASS’86 Ta Naira Miliyon 50, Muna Godiya Amadadin daukacin Kungiyar tsoffin daliban Makarantar Koyon Harkokin Kasuwanci ta Wudil WUCOBA CLASS’86 Da iyalansu baki na mika sakon Bangajiya tare da godiya ga Dan uwa kuma Amini, Alhaji Sayyu Idris Damtata Bisa gudunmawar Naira Miliyon 50 da ya Bayar domin rabawa abokan karatunsa na WUCOBA CLASS’86.
Babu shakka wannan Gudunmawa yazo Alokacin da ake bukatar ta musamman akwai daga cikin ‘yan Class’86 da suke cikin mawuyacin hali, don haka samun tallafin ya mutukar faranta mana Rai, don haka Muke isar da godiyar mu Alh Sayyu Idris Dantata tare da rokon Allah ya Ci gaba yalwata arzikinsa, ya kikan magabatansa ya tsare mana kuma da mituncin sa.
Sannan Muna fatan Alh. Sayyu Idris zai Ci gaba da irin wannan abin alhairin nan gaba domin karfafar mambobinmu domin saukakawa ‘yan uwa halin da ake cikiHakazalika wannan sakon godiya ba zai cika ba sai mun Mika irin wannan godiya ga Dan Uwa Mustapha Bala Dawaki tsohon Wakilin Al’ummar Kananan hukumomin Dawaki Kudu Da Warawa Wanda shima domin fatan ganin kowa ya samu wannan tallafin ya cika Naira Miliyon guda da doriya.
Muna godiya kwarai da gaske Bisa dawainiya da ake da abokan karatunmu.Alokacin guda kuma Muna kara godiya ga fitattu mambobin mu wadanda Suka Jima suna daukar nauyin abincin taro, biyan kudin dakin Taro da sauran hidindimun tarukanmu, Muna jinjana masu tare da rokon Allah yalwata arzikinsa.