
Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban Karamar Hukumar ta Minjibir Capt. Jibrin Nalado Aliyu ya ɗauki nauyin Ɗalibai ƴan asalin ƙaramar hukumar a yunƙurinsa na inganta harkokin kiwun lafiya a yankin.
A safiyar wannan rana ta Talata ne aka ƙadamar da miƙa takardun samun gurbin karatun ga ɗaliban da suka haɗar da Maza da Mata.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da Hon. Jibrin Nalado Alliyu ke ƙoƙarin ƙaddamar da rabon Kujerun zama ga makarantun yankin, a ƙoƙarinsa na magance matsalar Ilimi, a yankin.
 
         
         
         
         
        