Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta mika kwayoyi 450,000 na Pregabalin ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC), domin gudanar da binciken dakin gwaje-gwaje da kuma matakan doka.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a Kano, ACGN A. I. Ahmad, ya bayyana cewa an kama miyagun kwayoyin ne a cikin katuna 60 da aka lullube a mota, inda aka tare ta a kan hanyar Kano–Hadejia ba tare da takardun izini ba.
A lokacin karɓar kayan a Kano ranar Alhamis, Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta jinjinawa NDLEA bisa bin yarjejeniyar fahimtar aiki tare ta shekarar 2024, tare da tabbatar da ƙarin haɗin gwiwa don kare lafiyar al’umma.
Adeyeye, wadda Kwamishinan hukumar a Kano, Mista Kasim Ibrahim ya wakilta, ta ce za a gudanar da bincike a dakin gwaje-gwaje kan kwayoyin, bayan haka kuma a ɗauki matakan gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.