
Daga Saifullahi Gambo Minjibir
A yammacin Talata Wakilan Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II PhD CON, suka ziyarci ofishin sabon Kwaimishinan Shari’a Barrister Abdulkarim Maude SAN a domin tayashi murnar kama aiki.
Ziyarar ta ƙarkashin jagorancin babban Danmajalissar Sarkin Kano, kuma Matawallan Kano Alhaji Aliyu Ibrahim da kuma Sarkin Shanun Kano Alhaji Shehu Muhammad Dankadai.
A ziyarar tasu sun taya sabon kwamishinan murna tare da fatan aiki tukuru dan inganta fanninsa da nufin bunkasa cigaban jihar.
Daga karshe sun bayyana masa cewa Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya tayashi murnar kama aiki da fatan gamawa lafiya cikin Nasara.
mako guda ke nan da kama aikin na sabon kwamishinan Shari’a na jihar Kano wato Barrister Abdulkarim Maude SAN wanda ya zama kwamishinan Shari’a na farko mai lambar ƙwarewa ta SAN a tarihin jihar Kano.