
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano.
A ci gaba da Gudanar Shirin Koyawa Mata sana’un dogaro dakai Wanda Khadimul Nabiyi, Alhaji Kabiru Sani Kwangila ya dauki nauyin kuma hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Kasuwan Jihar Kano karkashin jagorancin Amb. Auwalu Gabari Jakada, a wannan makoma tawagar ta sauka a garin Tamburawa inda aka Kaddamar da Koyawa matan Karamar Hukumar Dawkin Kudu da Kura sana’u kala goma.
Da yake gabatar da jawabinsa Shugaban hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Kasuwan Jihar Kano Amb Auwalu Gabari Jakada ya bayyana matukar Farin Cikinsu Bisa ganin yadda mata suka fito domin koyi wadannan sana’u, sabida haka sai tabbatarwa da cewa yanzu haka cikin mat dubu 100,000 da akayi Alkawarin Koyawa Sana’un dogaro dakai a fadin Jihar Kano,yanzu haka an Koyawa Mata dubu 11,500.
Daganan sai ya buqaci matan da za’a Koyawa wannan sana’u su matar da hankali domin ganin sun koyi abunda Suka zo dominsa, ya ce tuni Kungiyar Tayi magana da Gwamnan Jihar Kano wajen neman ahigar da matan da akai yawa wannan sana’u cikinqadanda Gwamnan zai talkafawa a cikin ahirunsa na talkafawa Jama’ar Kano.

Alokacin Taron an Koyawa Mata sana’ar dinki iri daban daban da sana’ar Kitso da kunshin Wanda ma enko ba tada jari zata iya fara sana’ar dinki da kunshi da kuma yuraren fesawa, a karshe ya yi addu’ar fatan Allah ya karawa Alhaji Kabiru Sani Kwangila lafiya sannan ya jinjinawa Alhaji Munzali Sani Bisa Ci gaba da daqiniya da wannan aiki da Khadimul Nabiyi ya dauki nauyin gudanarwa.Cikin bakin da Suka halarvi wannan taro akwai Wakilin Dagacin Tamburawa, Sarkin Kasuwa, Sakataren Kungiyar ‘Yan Kasuwan Jihar Kano, masu unguwanni da sauran Al’ummar Kana hukumomin Dawaki Da Kura ne Suka halarvi Taron.