

Daga Saifullahi Gambo Minjibir.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barrister Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, Ya Miƙa Ta’aziyyarsa bisa Rasuwar ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano Biyu.
Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Hon. Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya karɓi labarin rasuwar wasu fitattun ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu da matukar alhini da bakin ciki.
Wannan dai na zuwa ne bayan samun labarin rasuwar, Honourable Sarki Aliyu Daneji, wakilin Mazabar Kano Municipal, da kuma Honourable Aminu Sa’adu Ungogo, wakilin Karamar Hukumar Ungogo, a majalisar dokokin jihar Kano.A madadin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Babban Lauyan Jihar yana bayyana tausayinsa da alhininsa na zuciya ga iyalan marigayan, tare da mika ta’aziyyar sa ga al’ummar kananan hukumomin da suka fito, da daukacin al’ummar Jihar Kano bisa wannan babban rashi.
Hon. Abdulkarim Kabiru Maude , SAN, ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ta musamman ga mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da dukkan ’yan Majalisun jihar Kano.
Zalika Kwamishinan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rasuwar wadannan ’yan majalisa masu kwazo, inda ya bayyana rashinsu a matsayin babban rashi ga Al’ummar jihar Kano.
Babban Lauyan Jihar Kano yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya gafarta musu, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu, ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, da daukacin al’ummar Jihar Kano haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi.