
Donnarumma Ya Koma Manchester City Daga Paris Saint-GermainManchester City ta kammala daukar mai tsaron ragar Paris Saint-Germain, Gigio Donnarumma, bayan cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa darajar cinikin ta kai tsakanin Yuro miliyan 30 zuwa 35, inda PSG ta amince ta rabu da dan wasan nata.Donnarumma ya sanya hannu kan dogon kwantiragi da City, kuma an tsara masa gwajin lafiya a yau kafin a kaddamar da shi a hukumance.
Sabon zuwan tsohon gwarzon Euro 2020 zai kara karfi a bangaren tsaron ragar kungiyar Pep Guardiola.