
Liverpool ta kammala daukar Alexander Isak daga Newcastle.
Tauraron dan wasan gaba na Newcastle, Alexander Isak, ya kammala shirin komawa Liverpool bayan an cimma matsaya tsakanin kungiyoyin biyu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Isak zai yi gwajin lafiya a yau, tare da sanya hannu kan kwantiragin shekaru shida wanda zai kare a shekarar 2031.
Liverpool za ta biya Fam miliyan £125, yayin da Newcastle za ta karɓi jimillar fam miliyan £130 bayan yarjejeniyar ta kammala.
Tuni kungiyoyin biyu sun riga sun yi musayar takardun yarjejeniyar a daren jiya, yayin da ake sa ran fitar da sanarwar ɗaukan ɗan wasan a hukumance daga Liverpool da Newcastle a yau.