Mai horaswa Justine Madugu, ya zaɓi Rasheedat Ajibade, Chiamaka Nnadozie, Francisca Ordega da Asisat Oshoala a cikin jerin ‘yan wasa 24 da za su fafata a Gasar Cin Kofin Mata ta Afrika karo na 13.
‘Yan wasan za su wakilci Super Falcons domin neman lashe kambun nahiyar karo na 10 a WAFCON ta 13 da za a gudanar daga ranar 5 zuwa 26 ga Yuli, a ƙasar Morocco.Sauran ‘yan wasan da aka zaɓa sun haɗa da Ashleigh Plumptre da Michelle Alozie, Osinachi Ohale da Deborah Abiodun, Jennifer Echegini da Christy Ucheibe.
Falcons za ta kara da Portugal a Lisbon ranar Litinin, sannan su fafata da Black Queens na Ghana a Morocco ranar Lahadi, 29 ga Yuni.
