
Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Kano Kan Rushe Shugabannin Jihar.Jam’iyyar NNPP ta kasa ta bayyana labarin da ke yawo na cewa wata kotu a jihar Kano ta soke rushe shugabannin jam’iyyar na matakin jiha, kananan hukumomi, da mazabu a matsayin “wasan kwaikwayo” da kuma take ka’idojin shari’a.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson ya fitar, ya bayyana cewa har yanzu ba su samu wata takarda daga kotu ba, don haka suke daukar labarin a matsayin “jita-jita.
Tushen Takaddamar:
Wannan martani ya biyo bayan rahotanni da suka karade kafafan yada labarai cewa wata kotu a Kano ta bayar da umarnin dakatar da rushe shugabannin jam’iyyar na Kano, biyo bayan wata karar gaggawa (ex-parte) da aka shigar gaban Mai Shari’a Nasiru Saminu a ranar Talata.
Sai dai jam’iyyar ta NNPP ta dage kan cewa ko da jita-jitar gaskiya ce, matakin ya saba wa ka’idojin shari’a da kuma misalan hukunci da aka riga aka kafa a baya.”Kotu Ba Ta Da Iko Kan Al’amuran Cikin Gida”Jam’iyyar ta bayyana cewa kuskure ne babba ga alkali ya ba da umarnin dakatar da matakin da tuni Kwamitin Aiki na Kasa ya riga ya kammala aiwatarwa.
Sanarwar ta kara da cewa:> “Wannan mataki ne haramtacce domin kotu ba ta da ikon shiga tsakanin al’amuran cikin gida na jam’iyya. Saboda haka, rushewar da aka yi wa shugabannin Kano a dukkan matakai tana nan daram.”>
Jam’iyyar ta kafa hujjoji da hukuncin Kotun Koli, inda ta bayyana cewa kotun kolin ta sha fadin cewa harkokin jam’iyya na cikin gida ne kuma kotu ba ta da hurumin tsoma baki a ciki. Ta kwatanta matakin kotun ta Kano a matsayin “rashin tarbiyya ta shari’a” idan har aka tabbatar da gaskiyar umarnin.
“Ya kara da cewa yayin da ake tunkarar, babban zaben shekarar 2027, NNPP ta yi kira ga jama’a da su sanya idanu kan bangaren shari’a, inda ta yi zargin cewa wasu ’yan siyasa na kokarin amfani da wasu alkalai wajen cimma burinsu na kashin kai.
Daga karshe, jam’iyyar ta yi gargadin cewa idan har aka tabbatar da wannan umarni, ba za ta yi wata-wata ba wajen shigar da koke gaban Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) domin hukunta duk alkalin da aka samu da hannu wajen bayar da irin wannan umarni na haramci.