Daga Ado Farin Gida
Gwamnatin Jihar Kano ta kuduri aniyar kafa wani Asusun Tallafi na Musamman domin taimaka wa jama’a, musamman waɗanda suka fuskanci bala’o’i da iftila’i a fadin jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai da Rage Radadi, Adamu Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin wani taron bita na yini guda da ya tattaro masana da kungiyoyin tallafi. Ya ce wannan asusu zai kasance karkashin kulawar kwamitin amintattu da kuma daraktan janar domin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Bugu da ƙari, kwamishinan ya bayyana cewa za a samar da rumbunan ajiye kayayyakin agaji a masarautu hudu da kuma shiyoyi uku na jihar, lamarin da zai ba da damar kai agaji cikin sauri ga jama’ar da abin ya shafa.
A nasa bangaren, Dr. Aminu Magashi Garba, wanda shi ne mai ba da shawara kan harkokin cigaba, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka sosai ganin girman jihar Kano da yawan jama’ar ta. Ya ce asusun zai zama hanya ta musamman wajen magance matsalolin da ke biyo bayan bala’o’i a jihar.