Ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi gargadi ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wasu ’yan siyasa da su guji kawo cikas ga babban taron ƙasa na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Birnin Ibadan, Jihar Oyo, ranar 15 ga Nuwamba, 2025.

Gwamnonin sun jaddada goyon bayansu ga kudirin da kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 101 ya cimma a watan Yuli 2025, kan shirye-shiryen taron ƙasa na PDP.
Gargadin ya fito ne daga wata sanarwa da aka fitar bayan taron gwamnonin karo na bakwai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ranar Asabar.
Taron wanda Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranta, ya mayar da hankali kan halin da ƙasa ke ciki, matsalolin tsaro, rushewar darajar dimokuraɗiyya da kuma shirye-shiryen taron ƙasa mai zuwa.