Ado Danladi Farin Gida, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da inganta manyan makarantu a fadin jihar domin samar da ingantaccen ilimi da cigaba ga matasa.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, kuma Kwamishinan Ilimi mai zurfi, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ne ya bayyana haka ne yayin kaddamar da taron shekara-shekara na 48 na shugabannin kwalejojin shari’a da addinin Musulunci na Najeriya (COPCLIS), wanda aka gudanar a Kwalejin Aminu Kano koyon ilimin shari’ar Addinin Musulunci ta (AKCILS).
Kwamared Gwarzo ya jinjinawa COPCLIS bisa rawar da take takawa wajen bunkasa ilimi, yana mai cewa tattaunawa da hangen nesan kungiyar na taimakawa wajen tsara makomar ilimi a Najeriya.
Ya yaba wa shugaban da ya kammala wa’adinsa bisa nasarar da ya cimma, ciki har da mayar da shirin Diploma na Shari’a zuwa matakin National Diploma, tare da shigar da shi cikin tsarin JAMB a shekarar 2024.
Mataimakin Gwamnan ya kuma taya sabon shugaban kungiyar COPCLIS, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, murna tare da bukatar ya ci gaba da kare martabar ofishin da kuma cimma manufofin taron.
Game da matsalolin gine-gine, Gwarzo ya tabbatar da cewa gwamnati tana daukar matakai don shawo kan su, inda ya bayyana cewa dokar da za ta mayar da AKCILS cikakkiyar Kwalejin Ilimi tana hannun Ma’aikatar Shari’a domin duba ta.
A nasa jawabin, Farfesa Jakada ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa tallafin da ta bayar, ciki har da gyaran dakin taro da wuta ta lalata da kuma daukar nauyin tantancewar NBTE. Ya bukaci karin taimako don gyaran dakunan karatu da suka lalace da kuma shigar da kwalejoji cikin shirin TETFund.
An karrama fitattun shugabanni da suka hada da Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo, Kwamishinan Ilimi Gwani Dr. Ali Haruna Makoda, da Kwamishinan Kimiyya da Fasaha Dr. Yusuf Ibrahim K/Mata saboda gudummawarsu wajen ci gaban ilimi a Kano.