Wani soja mai gabatar da ƙara a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya nemi kotu da ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Joseph Kabila, hukuncin kisa kan tuhumar cin amanar ƙasa da aikata laifukan yaƙi.

Janar Lucien Rene Likulia ne ya gabatar da wannan roƙo ga kotu, inda ya ce Kabila ya aikata laifuka masu tsanani da suka haɗa da tayar da tarzoma da kuma goyon bayan mayaƙan M23 da ake zargin Rwanda ke daukar nauyi.
Tsohon shugaban, wanda ya fara gurfana a gaban kotu tun watan Yuli, yana fuskantar ƙarin tuhumomi na haɗa baki wajen kifar da gwamnatin Shugaba Felix Tshisekedi, da kuma laifukan kisan kai, azabtarwa da fyade da ake danganta su da mayaƙan M23.