Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta fitar da sabon gargadi kan yiwuwar ambaliya a wasu yankunan Najeriya sakamakon karuwar ruwan Kogin Neja daga ɓangaren ƙasar Benin.

A sanarwar da aka fitar ranar Juma’a, hukumar ta umurci dukkan ofisoshinta da ke kusa da garuruwan bakin kogin da su ƙara wayar da kan jama’a da kuma kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana don guje wa asarar rayuka da dukiyoyi.
NEMA ta kuma shawarci mazauna yankunan da ke cikin haɗari da su koma wuraren da suke da kan tudu domin kare kansu daga ambaliya. Haka zalika ta bukaci gwamnatocin jihohi da kwamitocin kananan hukumomi su ɗauki matakan gaggawa na kariya.