Hukumar raya Kogunan Hadeja da Jama’are ta mikawa rundunar tsaro mai kare fararen hula da kadarorin al-umma sabuwar makarantar horas da Jami’anta da gwamnatin tarayya ta samar a karamar hukumar Gwarzo dake jihar Kano.

A yayin mika ginin bayan kammalawa, Shugaban hukumar Hadeja Jama’are, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda ya samu wakilcin daraktan mulki da kudi, Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da ingancin ginin, yana mai cewa samar da makarantar zai taimakawa mutanen yankin..
Anasa bangaren, Yusuf Tabuka, wanda ya wakilci Mataimakin shugaban majalissar dattijai, Sanata Barau Jibrin, wanda ya kawo aikin makarantar a mazabarsa ta Kano ta Arewa, yace za su cigaba da gine-gine a makarar nan bada jimawa ba…
A ƙarshe, babban kwamadna Janar na Hukumar Civil Defense na kasa, Ahmad Audi wanda ya samu wakilcin, Shafi’u Abdulmumin Dayi, ya yaba da gudummawar da aka baiwa hukumar, yana tabbatar da cewa makarantar zata bunkasa kwarewa da kwazo na Jami’an rundunar.