Kungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha ta Ƙasa (ASUP) ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki idan gwamnatin tarayya ta kasa biyan bukatunta cikin kwanaki 21 masu zuwa.

Jami’in kungiyar na shiyyar B, Innocent Simji, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, inda ya ce matakin ya yi daidai da matsayar da uwar kungiyar ta dauka.
Simji ya ce an dauki wannan mataki ne bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar kungiyar da aka gudanar a Abuja ranar 14 ga watan Agusta.
Ya kuma ce gargadin ya biyo bayan yadda gwamnati ta kasa magance muhimman matsalolin da ke addabar kwalejojin fasaha a fadin kasar.