Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 27, Umar Adamu Umar, daga karamar hukumar Fagge, Jihar Kano, dauke da kilogiram 9 na tabar wiwi (Colorado) a hanyar Zariya zuwa Kano.

Jami’an hukumar sun gano cewa ya rarraba tabar wiwin cikin fakiti 19, inda aka cafke shi ranar 6 ga Agusta, 2025, yayin da yake yunkurin jigilar kayan daga Legas zuwa Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa darajar kayan a kasuwa ta haura Naira miliyan 10, lamarin da ya haifar da babbar asara ga masu safarar miyagun kwayoyi.
Shugaban rundunar NDLEA na Kano, ACGN A.I. Ahmad, ya ce za su ci gaba da kai hare-hare da sintiri domin hana shigowa da irin wadannan kwayoyi cikin jihar