
Taron ya gudana a safiyar wannan rana a fadar shugaban kasa, domin tattaunawa kan tsare-tsare da aiwatar da shirin ciyar da ɗaliban makarantu a Nigeria wato (Home-Grown School Feeding Programme (HGSFP).
Taron wanda aka shirya shi karkashin jagorancin ActionAid Nigeria, da Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, da kuma shirin nan na Renewed Hope, National Home-Grown School Feeding Programme (RH-NHGSFP), Ma’aikatar Jin Kai da Rage Talauci (FMHPA), Ma’aikatar Aikin Gona da adana rumbun Abinci (FMAFS), da Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF).
Haka kuma taron ya samu goyon bayan World Food Programme (WFP), WACHEF, da kuma taimakon kudi da na fasaha daga ECOWAS da Hukumar Cigaban Kasashen Ketare ta Spain (AECID) karkashin SPAC-West Africa Project.
Zalika taro ya halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Andrew Mamedu (Daraktan ActionAid Nigeria), Dr. Princess Aderemi Adebowale (Shugabar RH-NHGSFP), Dr. Nuruddeen Abubakar Zauro (Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki da kuma Sunusi Musa SAN (Shugaban Institute of Peace and Conflict Resolution), Dr Abubakar Ibrahim Kunya.

A tattaunawar, mahalarta taron sun bayyana cewa shirin ciyar da dalibai abinci a makarantu zai taimaka wajan:Inganta lafiyar yara da kaifin ƙwaƙwalwa.Tallafawa kananan manoma.
Tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa da adalci a kasa.
An bayyana wannan shiri a matsayin wata muhimmiyar hanya da za ta taimaka wajen saukaka talauci, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar hada kan bangarori daban-daban na gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa.