
Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa da Kasa (IHRC-RFT), reshen Najeriya, mai matsayin shawara na musamman a gaban Majalisar Dinkin Duniya (ECOSOC Special Consultative Status), ta bayyana matsanancin damuwa kan yadda ake yawan yin amfani da Court order amatsayin hanyar kaucewa hukunci da kuma kaucewa bincike bayan aikata zalunci ko cin zarafi.
Lamarin ya zama ruwan dare a Nigeria la’akari da yadda wasu masu laifi ke gaggauta samun Court order domin hana jami’an tsaro cafke su ko gudanar da bincike a kansu.
Wannan mummunan dabi’a ta lalata amincin tsarin shari’a, ta rage karfin hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu, sannan ta raunata amincewar jama’a ga doka da oda.
Da dama daga ma’aikatan tsaro da wasu alkalan kotu na cikin masu kyamatar wannan katoɓara.
IHRC-RFT ta bayyana cewa ba ta yi kira da a haramta Court order gaba daya ba. Abin da muke nema shi ne a tabbatar cewa ana bayar da irin waɗannan umarni bisa adalci, gaskiya da daidaito –ta yadda ba za a bar wani ya yi amfani da doka a matsayin makami na tauye wa ‘yan kasa hakkinsu ba.
Wannan cin zarafin tsarin shari’a ya sabawa yarjejeniyar kare hakkin dan adam ta duniya (Universal Declaration of Human Rights –UDHR), musamman:Sashe na 7: “Duk mutane daidai suke a gaban doka, kuma suna da hakkin kariya daga wariya a kowane hali.”Sashe na 8: “Kowane mutum yana da hakkin samun cikakkiyar kariya daga kotunan kasa masu iko idan aka take masa hakkin da kundin tsarin mulki ko doka ta ba shi.”A matsayin wani mataki na fafutuka, IHRC-RFT ta riga ta aika wasika zuwa ga Ministan Shari’a da Babban Mai Shari’a na Kasa (Chief Justice of Nigeria) domin su:
1.Gudanar da bincike cikin gaggawa kan yadda ake amfani da umarnin kotu Court order ta hanyar da ba ta dace ba a fadin kasar nan.
2. Karfafa matakan kariya domin tabbatar da cewa umarnin kotu ba sa zama kayan hana adalci.
3. Hada kai da majalisar dokoki, bangaren zartarwa da hukumomin tsaro don kare mutuncin tsarin shari’ar Najeriya bisa ka’idojin kare hakkin dan adam na duniya.
IHRC-RFT ta bakin shugaban ta, Amb. Abdullahi Bakoji AdamuDaraktan Kasa, IHRC-RFT Nigeria Chapter(Mai matsayin ECOSOC Special Consultative Status, Majalisar Dinkin Duniya, ya jaddada cewa wajibi ne a dauki mataki cikin gaggawa domin dawo da amincewar jama’a ga tsarin shari’a na Najeriya da kuma tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da mutunta hakkokin dan adam da martabar kowane dan kasa.