Ado Danladi Farin Gida-Kano
A wani mataki na samar da zaman lafiya da rage laifuka a jihar Kano, mutane 900 da suka kasance cikin harkar tada zaune tsaye sun ajiye makaman su tare da rungumar shirin Safe Corridor da gwamnatin jihar ta ƙaddamar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da alkawuranta na samar musu da ayyukan yi da horo na sana’o’i, don kada su koma kan tsohuwar rayuwar laifi.
Babban Kwamandan Hukumar Hisba, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da cewa hukumar za ta saka su cikin shirin auran yar gata, tare da jan hankalin iyaye da su daina la’antar ‘ya’yansu saboda hakan kan jefa su cikin matsaloli.
Wasu daga cikin tsoffin ‘yan daban sun bayyana farin cikinsu, tare da kudurin zama mutanen kirki da zasu bayar da gudummawa ga al’ummarsu.
 
         
         
        