
Daga Aliyu Samba
Rahoton tsaro daga Ma’aikatar Harkokin Tsaro ta Cikin Gida a Jihar Katsina, ya nuna cewa kananan hukumomi 12 daga cikin 24 na jihar sun samu cikakken kwanciyar hankali, yayin da wasu uku ke ci gaba da fuskantar barazanar ‘yan bindiga.
Rahoton ya bayyana cewa cikin kananan hukumomin da aka tabbatar da zaman lafiya har da Safana, wacce ta shiga jerin ragowar a kwanan nan. Sauran sun haɗa da Jibia, Batsari, Dammusa, Katsina, Batagarawa, Charanchi, Bindawa, Ingawa, Kafur, Danja da Kusada. A cewar rahoton, a waɗannan yankuna ba a samu wani rahoton harin ‘yan bindiga ba a kwanan nan.
Haka kuma, rahoton ya ce kananan hukumomi tara sun samu ingantuwar tsaro, inda barazanar ke takaituwa ga wasu kauyuka na nesa kaɗan.
Wannan ya haɗa da Malumfashi, Kurfi, Dutsinma, Kankia, Musawa, Bakori, Funtua, Sabuwa da Dandume.
Sai dai rahoton ya nuna cewa Faskari, Kankara da Matazu suna cikin rukunin “waɗanda za su iya fuskantar barazana”, inda ake ci gaba da samun hare-haren ‘yan bindiga. Rahoton ya ce gwamnati da hukumomin tsaro suna ƙara zage damtse wajen magance matsalar.
A cewar ma’aikatar, sama da kashi 87 cikin 100 na kananan hukumomin Katsina na kan hanya mai kyau ta samun zaman lafiya, lamarin da ya nuna cewa ana samun ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.