
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana zaben cike gurbin ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara na mazabar Kauran-Namoda ta Kudu a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon samun matsaloli wasu rumfunan zaɓe guda biyar.
Baturan zaɓen yankin, Farfesa Lawal Sa’adu daga Jami’ar Tarayya ta Gusau, ya ce matsalolin da aka samu a gundumomin Sakajiki da Kyambarawa ne suka sa aka soke zaɓen.
A cewar Farfesa Sa’adu, tazarar kuri’u tsakanin jam’iyyu biyu da ke kan gaba—wato All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP)—ta kai kuri’u 1,662.
Wannan kuwa ya yi ƙasa da adadin katin zabe na dindindin (PVC) da aka karɓa a rumfunan da matsalar ta shafa.
Ya bayyana cewa a gundumar Sakajiki (lamba 06), rumfunan zabe guda biyu da ke da masu kada kuri’a 1,357 da kuma PVC 1,298 sun shiga cikin matsalar.
Haka kuma a gundumar Kyambarawa (lamba 05), rumfunan zabe guda uku da ke da masu kada kuri’a 4,088 da PVC 1,964 sun shiga ciki. Jimillar PVC da aka karɓa a rumfunan biyar da abin ya shafa ta kai 3,265.
Sakamakon da aka sanar kafin haka ya nuna jam’iyyar APC na kan gaba da kuri’u 7,001, yayin da PDP ta samu kuri’u 5,339.Yayin bayyana dalilin yanke hukuncin, Farfesa Sa’adu ya ambaci tanade-tanaden dokar zabe ta 2022—sashe na 24 (2&3), sashe na 47 (3), da kuma sashe na 51 (2)—inda ya ce hukumar ba ta da wani zaɓi illa bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
INEC ta ce za ta sanar da sabon ranar gudanar da zaben maimaitawa a rumfunan da abin ya shafa nan gaba.