Al’umma sun shiga wani irin yanayi bayan yan bindiga sun kai wani hari a birnin Lafia. Majiyoyi sun ce yan bindiga da ake zargin barayi ne sun yi garkuwa da hadimin tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura.
Rahoton Zagazola Makama ya ce maharan sun dauke Alhaji Adamu a jiya Juma’a 15 ga watan Agustan 2025 a jihar Nasarawa
Tsohon gwamna, Umaru Tanko Al-Makura ya mulki jihar Nasarawa daga shekarar 2011 zuwa 2019 karkashin CPC kafin a hade ta dawo APC a 2014. Al-Makura ya kasance daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa a 1998 shekara daya kafin dawowa mulkin dimokuraɗiyya.
