
Daga Saifullahi Gambo Minjibir
Jagoran kwankwasiyya a ƙaramar Minjibir Hon A A Abdulhamid shi ne ya jagoranci Al’ummar zuwa ga jagoran ɗariƙar kwankwasiyya na ƙasa, wato Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganawar na zuwa ne yayin da Al’ummar ta karamar hukumar Minjibir ke halartar taron karɓar lambar ƙwarewa ta S.A.N da Barrister Abdulkarim Maude ya samu.
A yayin ziyarar Sanata Kwankwaso ya yabawa A’ummar yankin na Minjibir bisa goyan bayansu ga tsarin kwankwasiyya.A Safiyar lahadin nan ne gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya aike da sunan Barrister Abdulkarim Maude ga zauren Majalisar Dokokin Kano, domin tantance shi a matsayin sabon kwamishinan Shari’a na jihar Kano.

Ganawar dai ta samu halartar gwamman matasa, dattawa da kuma jagoran ɗariƙar kwankwasiyya na Minjibir Hon. A A Abdulhamid wanda shi ne mai wakiltar Minjibir a zauran Majalisar Dokokin Kano, sai shugaban ƙaramar hukumar Minjibir Capt Jibrin Nalado Alliyu da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Minjibir.