
Jam’iyyar ta NNPP) reshen jihar Kano ta kori dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, daga jam’iyyar bisa zargin aikata ayyukan da suka saba wa manufar jam’iyya da kuma kin biyan kuɗaɗe.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashim Sulaiman Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar.
Zarge-zargen da aka yi masa
Dungurawa ya ce an dauki matakin ne sakamakon yadda Kofa ya ci gaba da bayyana ra’ayoyi a kafafen yada labarai da suka saba wa jam’iyyar da shugabancinta.Ya kuma bayyana Kofa a matsayin “dan siyasa marar karfi” wanda nasararsa ta lashe kujerar majalisar wakilai ta faru ne kawai da taimakon tafiyar Kwankwasiyya da kuma dandalin NNPP, ba wai da karfin kansa ba.“Da gaske yana da tasiri a siyasa, da tuni ya ci zabe a karkashin APC, amma ya gaza. Sai bayan da ya shiga NNPP ta hannun Kwankwasiyya ya samu nasara.
Yanzu kuma yana yaudarar kansa yana ganin shi mai karfi ne,” in ji Dungurawa.
Kwamitin sasanci.
Shugaban jam’iyyar ya ce an kafa wani kwamiti na sasanci domin tattaunawa da Kofa bayan hirar sa da gidan Talabijin na Channels Television.
To sai dai Kofa ya sake irin waɗancan maganganun a wasu kafafen yada labarai wanda hakan ke tabbatar da cewa ya kauce daga tafarkin jam’iyyar NNPP.
Dungurswa ya kara da cewa “maimakon Kofa ya amince da tattaunawar sai ya ci gaba da yin aiki da ya saba wa muradunmu, inda har ya bayyana biyayya ga wani bangare a wajen jam’iyyar, wanda hakan ne ya sa muka yanke shawarar korar shi, yanzu bashi da wata ƙima da zai kara mana,” in ji shi.
Batun kudaden wajibci
Dungurawa ya kuma zargi Kofa da kin biyan kudaden wajibci na jam’iyya, inda ya sha alwashin cewa NNPP za ta kai shi kotu domin karbo hakkinta.
Batun komawa APC
Game da rade-radin cewa Kofa na iya komawa jam’iyyar APC, shugaban NNPP a Kano ya ce hakan ba zai rage karfin jam’iyyar ba, yana mai jaddada cewa siyasa lamari ne na hadin gwiwa da kungiyoyi, kuma Kwankwasiyya na nan daram tare da jagoranta, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.