
Al’ummar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo sun bukaci mahukunta a matakin Kasa da jihar Kano su taimaka domin gyara hanyar da ta hada kananan hukumomin biyu.

Al’ummar wannan yanki sun shaidawa wakilinmu cewa matukar aka samu damar gyara hanyar, to zata inganta tattalin arzikin yankin tare da saukakawa al’ummar yankin wajan sufuri.
Sai dai sun bayyana takaicinsu dangane da yadda shugabanni a matakai daban-daban suka dade suna musu alkawarin wanna hanya, wanda daga bisani kuma sai kaji tamkar an aiki bawa garinsu.
Lalacewar hanyar ta Ungogo zuwa Minjibir na cigaba da haifar da jikkatawa, tare da mutuwar Al’ummar yankunan ciki kuwa harda Mata masu juna biyu.
Al’ummar dai sun bukaci Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba K Yusuf da ya kawo musu dauki domin gyara musu wannan hanya ta Minjibir zuwa ungogo domin taimakon mutanen da suke wannan yanki.