
Saifullahi Gambo Minjibir
Dakarun Rundunar 3 Division tare da haɗin gwiwar Joint Task Force Operation Enduring Peace (JTF OPEP) sun yi nasarar kwato makamai da harsasai a wani samame da suka kaddamar kan maboyar wani sanannen dillalin makamai a Jihar Filato.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, aikin ya gudana ne da safiyar Litinin a ƙauyen Kurra Berom da ke cikin Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi, bayan samun ingantaccen bayanan sirri daga jami’an tsaro.
Ababen da aka samu sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya, mazagunan AK-47 guda biyu da kuma harsasai na musamman kalib 7.62mm guda 38.Sai dai kafin isowar dakarun, waɗanda ake zargi sun arce daga maboyar, lamarin da ya hana cafke su a wajen.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike tare da farautar waɗanda suka tsere, tare da tabbatar da aniyarsu na ci gaba da murkushe harkar safarar makamai da kuma kare yankin daga duk wani barazanar tsaro.