.

Abinda yasa muka dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano “Majalisar Dokokin Kano.
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano Muhammad Naziru Ya’u na tsawon wata 3 ne.
Rahotanni sun ce Majalisar Dokokin ta daukin matakin ne, Sakamokon bullar rahotanni dake nuni da zargin al’mundahana da kuma rashin tabuka abun azo a gani.
Zalika ana zargin Hon Naziru da almundahana wajen sayar da takin zamani da jihar kano ta bawa Shugaban domin siyar wa manoman yankin a farashi mai rahusa.