Daga – Ado Ɗanladi Farin Gida, Kano
Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta yi kira ga gwamnonin yankin Arewa da ‘yan majalisar tarayya da su haɗa kai wajen dawo da martabar yankin da kuma magance matsalolin tsaro da rashin aikin yi da ke damun matasa.

Shugaban amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu, ya yi wannan kira a taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka yi a Kano, inda ya jaddada muhimmancin shugabannin siyasa su mayar da hankali kan dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shima shugaban ACF na Kano, Dr. Gwani Farauk Umar, ya bayyana fatan da na ganin an kawo ƙarshen matsalolin daba da shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar Kano, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare matasa daga fadawa cikin halaka.