
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace fasinjoji tara a wani harin kwantan bauna da suka kai akan hanyar Itobe zuwa Anyagba da ke jihar Kogi.
Rahoton da Skm Hausa ta samu ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a kusa da Ogbabo Junction, lokacin da maharan suka fito daga daji tare da bude wuta a kan wata motar fasinja mallakin Peace Mass Transit.
Wata majiya ta shaida cewa direban motar, Mista Sunday Okechi, tare da wasu fasinjoji shida sun samu nasarar tserewa daga harin, yayin da sauran tara suka shiga hannun maharan, waɗanda suka kutsa da su cikin daji.
Bayan faruwar lamarin, tuni jami’an tsaro suka garzaya wajen da lamarin ya faru, inda suka kwashe motocin zuwa wani bigire na daban, domin tabbatar da tsaro.
A halin yanzu, jami’an tsaro tare da haɗin guiwar ’yan sa kai na Vigilante da kuma mafarauta sun fara aikin ceto domin kubutar da waɗanda aka sace da kuma kama masu laifin.