Daga Ado Ɗanladi Farin Gida, Kano
Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Ƙasa da Ƙasa (IHRC) ta ce duk direban da ya haddasa mutuwa ta hanyar amfani da aron lasisin tuki a aron hannu zai fuskanci doka, ciki har da tilasta biyan diyya ga iyalan mamata.

Mataimakin shugaban hukumar a Najeriya, Ambassador Dr. Abubakar Rabo, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke titin Court Road, Kano.
Ya ce IHRC ta samu lasisi daga Majalisar Dinkin Duniya domin bin sahun irin waɗannan hadurra da suka yi sanadin mutuwar fasinjoji, yana mai cewa ba za a bar lamarin haka kawai ba.
“Ko direban ya rasu a hadarin, za mu tabbatar an samu diyyar daga iyalansa. Babu wanda zai kashe rayuka sannan ya tafi salin alin,” in ji shi.
Dr. Rabo ya ce lokaci ya wuce da za a ci gaba da zura ido direbobi suna haddasa mutuwa ta hanyar tuki da aron hannu ko rashin kwarewa.
Hukumar ta kuma bukaci FRSC da kungiyoyin direbobi su kara himma wajen fadakar da mambobinsu game da hatsarin amfani da lasisin bogi ko wanda ba nasu ba.
“A mafi yawancin lokuta, irin wannan tuki da aron hannu ne ke haddasa hadurra, musamman a jihar Kano,” in ji shi.
Ya bayyana takaicinsa kan mutuwar wasu ‘yan wasan Kano a kwanakin baya da suka gamu da ajali a kusa da birnin Kano, sakamakon irin wannan tuki na rashin bin doka.