
Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa da yammacin Laraba, bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa don gano rawar da ya taka a belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan sauyi ana kallonsa a matsayin wani babban mataki wajen ƙarfafa ɗabi’un gaskiya, da rikon amana a wannan gwamnati.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Kwamishina Namadi ya bayyana cewa murabus ɗinsa na da nasaba da bukatar kare muradun al’umma da kuma la’akari da mahimmancin batun.
Ya ce: “A matsayina na ɗan gwamnati da ke gaba da gaba wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi, dole ne in ɗauki wannan mataki — kodayake yana da ɗaci. Duk da cewar ina da yakinin ba ni da laifi, ba zan iya watsi da tasirin yadda jama’a ke kallon lamarin ba, da kuma buƙatar kare ƙimar da muka gina tare.
”Alhaji Namadi ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yin hidima wa jiharsa, tare da sake jaddada jajircewarsa wajen gudanar da shugabanci na gari da rikon amana.
Ya ƙara da cewa:“A matsayina na nagartaccen ɗan ƙasa, dole ne in tsaya tsayin daka wajen kare amana da hangen nesa da muka gina a jihar nan. Zan ci gaba da kasancewa cikin masu biyayya ga akidar da ta kawo wannan gwamnati kan mulki.
”A nasa bangaran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin girmamawa, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba. Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba wajen yaƙi da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran ɗabi’un banza da ke lalata rayuwar matasa da al’umma gaba ɗaya.
Gwamnan ya kuma shawarci dukkan masu rike da mukaman siyasa da su rika taka-tsantsan a kan duk wani lamari da ya shafi jama’a, tare da neman izini daga hukumomin da suka dace kafin su tsoma kansu cikin irin waɗannan batutuwa.