
Bello Turji, Ya Amince da Yarjejeniyar Zaman Lafiya tare da Sakin Mutane 32 da ya yi Garkuwa da su, bayan gudanar da jerin zaman tattaunawa da wasu manyan malamai a sansaninsa da ke cikin dajin Fakai, a Jihar Zamfara.
Malamin addini mai tasiri, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, shi ne ya bayyana hakan yayin wata mahangar addini da aka gudanar a garin Kaduna a ranar Litinin.
A cewar Sheikh Musa, an gudanar da zaman sulhun ne sau uku a cikin watan Yuli, inda shugabannin ’yan bindiga suka amince da shirin zaman lafiya, ciki har da mika wasu daga cikin makaman da ke hannunsu.Sheikh Musa ya ce al’ummar Shinkafi ne suka roki malaman da su shiga tsakani domin a samu damar komawa gonaki ba tare da tsoron hare-haren ’yan bindiga ba.
“Mun gana da Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Sun amince da shawarwarin zaman lafiya. Sun kuma saki mutane 32 da suka hada da mata da yara da suka shafe kusan wata hudu a sansaninsu. Wasu daga cikin matan ma sun haihu a can, yayin da daya daga cikin fursunonin ya kamu da cizo daga maciji.
”Malamin ya ce makaman da ’yan bindigar suka mika sun hada da bindigogi da harsasai, kuma an amince cewa Fulani za su rika shiga gari ba tare da tsangwama ko hare-hare daga vigilante ba.
Ya kuma nuna wani bidiyo da ke nuna halin da wadanda aka sako suka tsinci kansu a ciki, da kuma wahalhalun da suka sha kafin su isa sansanin Turji.
Tuni al’ummar Shinkafi suka fara komawa gonaki da fatan dawowar zaman lafiya mai dorewa.