Yanzu haka tuni aka fara gabatar da kaso na farko kan horar da iyaye mata da yan mata noman zamani wato Green house, wanda ya gudana a Karamar Hukumar Minjibir.

Hon A A Abdulhamid ya bayyana cewa bayan samun horon, iyaye matan zasu amfana da tallafin Iri me inganci tare taki wanda zasu raini shukar da shi.
Hon Minjibir wanda shi ne Dan majalisa mai wakiltar Minjibir a zauran majalisar dokokin jihar Kano, ya ce shirin zai inganta tattalin arzikin matan da ma yankin karamar hukumar ta Minjibir.

A horon dai matan zasu koyi noman lambu wanda za su yi a cikin gidajensu, wanda zai basu damar noma Irin Tattasai, Dankalin Turawa, Tumaturi, Albasa, Barkono, Kabeji, da dai sauran naukan kayan lambu.A karshe ya bukaci matan da zasu amfana da wannan shiri su tabbatar sunyi amfani da horon da suka samu domin tafikar da rayuwarsu da ta iyalansu.
