Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a Sabon Garin Damri da ke karamar hukumar Bakura, Jihar Zamfara, a daren Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutane 70 ne aka sace a harin.Shaidu sun ce maharan sun shigo kauyen ne a kan babura tare da fara harbe-harbe ba tare da tantance kowa ba.
”Wannan mummunan al’amari ya faru ba tare da wani tallafi ba. Sun sace ’ya’yanmu da matanmu. Har yanzu babu wani labari daga gare su,” in ji wani mazaunin kauyen, Isa Sani, a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin.
Wani mazaunin da matarsa ta shiga cikin wadanda aka sace, ya shaida cewa ya tsira ne da kyar daga harin.Karamar hukumar Bakura na daya daga cikin wuraren da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga a Zamfara.
Yankin na iyaka da Jihar Sakkwato kuma yana kusa da dajin Gundumi, wanda aka dade ana alakanta shi da sansanonin shugabannin ’yan bindiga.Hare-haren ’yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya sun hada da sace mutane domin karbar kudin fansa, kisa, fashi da makami, farmaki a makarantu, masallatai, tare da kakaba haraji ga mazauna karkara.
Masana da masu sa kai sun bayyana cewa, ayyukan ’yan bindigar sun haifar da gagarumin rikicin jin kai, inda mutane sama da miliyan daya suka rasa matsugunansu, yayin da dubban wasu suka rasa rayukansu cikin shekaru kalilan da suka gabata.
Bincike ya nuna cewa rashin tsaro ya sa mutane da dama sun daina zuwa gonakinsu, wanda ke barazana ga abinci da zaman lafiya a yankin.
