Nigeria Babbar kotun tarayya dake Minnan Jihar Neja ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekara guda ko tarar naira dubu ɗari-ɗari saboda hako ma’adanai ba tare da lasisi ba.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da hukumar EFCC shiyyar Kaduna ta fitar, inda ta ce kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Abdullahi M. Dan-Ige ta yanke wa Yusuf Amadu, Babila Sani, Ibrahim Umar, Ephraim Jonas Okoro da Saidu Mohammed hukunci bisa amsa laifinsu.
EFCC ta bayyana cewa an kama su ne a yankunan Minna da Kateregi ta Karamar Hukumar Kacha, bisa bayanan sirri da suka tabbatar suna gudanar da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ciki har da duwatsu masu daraja.
Lauyan EFCC K.S Ogunlade ya roƙi kotun da ta yanke musu hukunci, yayin da lauyoyin da ke kare su suka nemi a sassauta musu bisa cewa sun nuna nadama.Kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara guda ko tara ta naira dubu 100 kowannensu.
