Wasu dalibai daga makarantun sakandaren Larabci a Jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan jinkirin da aka samu a alkawarin da Gwamnatin jihar ta dauka na tura su kasashen waje domin ci gaba da karatu.

Daliban sun ce tun shekara guda da ta gabata aka fara tsarin tantancewa daga makarantu da kananan hukumomi, inda aka zabi wadanda suka cancanta daga cikinsu don a tura su zuwa Jami’ar Kasar Masar. Sai dai har yanzu ba su samu damar tafiya ba, kuma babu wani bayani na gaskiya daga bangaren gwamnati.
Wani daga cikin daliban ya ce:
“Mun bi dukkan matakan da aka shimfida, an tabbatar da cancantar mu, amma daga nan sai shiru. Har yanzu muna jiran cikar wannan buri da muka jingina rayuwarmu da shi.”
Da wakilin SKM Hausa, ya tuntubi Ko’odineta na Qur’anic and Islamic Education a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Dr Abdulkadir Sani Aliyu Kurawa, don jin matsayar gwamnati a kan lamarin. , ya bayyana cewa jinkirin ya biyo bayan tafiyar gwamna zuwa aikin Hajji. Ya kara da cewa ana sa ran kafin karshen watan Oktoba, komai zai koma kan turbar da aka tsara.
“Mun san daliban na cikin damuwa, amma gwamnati na kan shirin tabbatar da alkawarin da aka dauka. A yanzu haka muna da yakinin cewa kafin karshen Oktoba, shirin zai fara aiki,” in ji Dr Kurawa.
Masu fashin baki na ganin cewa cikar wannan shiri zai taimaka matuka wajen bunkasa ilimin harshen Larabci a jihar, tare da ba matasa damar koyo a matakin kasa da kasa.