Rundunar Sojin Saman Najeriya karkashin Operation HADIN KAI (OPHK) ta kaddamar da wani gagarumin farmaki da ya yi sanadin hallaka wasu manyan kwamandoji da mayakan kungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

A cewar Air Commodore Ehimen Ejodame, Daraktan Hulda da Jama’a da Bayanin Sirri na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), wanda ya fitar da sanarwa a ranar Litinin, an kaddamar da harin ne a ranar Lahadi a Arina Woje, wani sansanin ISWAP da ke Kudancin Tumbuns a Jihar Borno, wanda aka fi sani da mafakar shugabannin ‘yan ta’adda.
Ejodame ya bayyana cewa an gudanar da farmakin ne bayan samun bayanan asiri da bibiya (ISR) da suka tabbatar da cewa wasu manyan ‘yan kungiyar ISWAP sun sake dawowa yankin bayan wasu rikice-rikicen cikin gida da suka faru a cikin kungiyar.
Rahoton farko na kimanta barnar yakin (Preliminary Battle Damage Assessment) ya nuna cewa an lalata gine-ginen shugabannin ISWAP, mayakansu da wuraren ajiye kayayyaki, wanda hakan ya janyo tsaiko da cikas ga shirin kungiyar na ci gaba da kai hare-hare da kuma samun kayan aiki a yankin.
Wannan nasara na daga cikin matakan da rundunar sojin Najeriya ke dauka domin murkushe ragowar ‘yan ta’adda da ke kokarin kafa sansanoni a yankunan da aka riga aka kwace daga hannunsu.