Zarge-zarge masu nauyi na tsangwama sun sake tasowa a gidan rediyon BBC, bayan da tsohuwar ma’aikaciyar gidan, Halima Umar Sale, ta bayyana irin abubuwan da ta fuskanta lokacin tana aiki da su.

Halima ta bayyana hakan ne a wani shiri na musamman da aka watsa a kafar talabijin ta Arewa24, inda ta ce ta fuskanci matsin lamba a bakin aiki.
Tsohuwar ma’aikaciyar ta ce abubuwan da suka faru da ita sun shafi tsangwama, nuna wariya, da rashin adalci a wurin aiki, amma ta jima tana boye su .
Idan za a iya tunawa, ashekarun baya, daya daga cikin wakilan BBC a Arewacin Najeriya ya yi jerin rubuce-rubuce a shafinsa na Facebook, yana bayyana irin matsalolin da ya fuskanta da kuma yadda aka tursasa masa barin aikin.
Wannan sabon zarge-zarge na Halima ya sake tayar da muhawara a shafukan sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra’ayoyinsu kan yanayin aikin da al’adar cin zarafi a wasu manyan kafafen watsa labarai.
BBC dai ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan zarge-zargen da aka yi a yanzu ba, amma akwai yiwuwar hakan zai tilasta kamfanin ya gudanar da bincike ko ya fuskanci tambayoyi daga hukumomin kula da ayyukan kafar.