Dakarun sojin Najeriya sun samu nasara a wani samame da suka kai kan ƴan bindiga a kauyen Warari, da ke karamar hukumar Rijau, jihar Neja, inda ta kashe da dama daga cikin su.

Harin, wanda ya faru a daren 22 ga Yuli da misalin 7:20 na yamma, ya samu tabbataci daga ‘Yan Sanda na Yankin Kontagora, wanda suka bayyana cewa an gudanar da luguden wutar ne tsare tare kuma cikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro.
Ƴan bindigar da aka yi artabu da su ana zargin ”yan wata ƙungiya da ke addabar yankin Neja zuwa Kebbi, kuma an ce artabun ya ɗauki sa’o’i kafin sojoji su samu galaba.
Majiyoyi sun ce “adadi mai yawa na ƴan bindiga an hallaka su,” sai dai ba a bayyana takamaiman adadin ba.
A yayin fafatawar, soja ɗaya ya rasu, a cewar rahotanni daga rundunar tsaro.
Daga bisani, hukumomi sun kara sanya yankin cikin tsauraran matakan tsaro, tare da ci gaba da aikin sintiri da leƙen asiri domin hana ramuwar gayya da kamo sauran barayin da suka tsere.