Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa wasu ƴan bindiga biyu sun rasa rayukansu a harin kwanton-bauna da wasu mafarauta suka kai a kusa da Gusau, babban birnin jihar.

Lamarin, wanda ya faru a ranar 22 ga Yuli, ya auku ne tsakanin kauyukan Fegin Mahe, Chuna, Kanawa da Gundumau, inda mafarautan da suka fito daga Mada suka yiwa ƴan bindigar kwantan bauna.
Kisan ƴan bindigar biyu ya haifar da fargaba sosai a kauyukan yankin, inda mazauna kauyukan da ke makwabtaka da wurin suka fara gudun hijira zuwa garin Mada, domin tsoron ramuwar gayya daga ƴan ta’addan da suka rage.
Wasu ma sun nufi Gusau, inda suka gudanar da zanga-zanga a gaban Gidan Gwamnatin Jihar, suna riƙe da alluna masu ɗauke da sakonni na neman kariya daga gwamnati.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya ce an dauki matakan gaggawa, ciki har da rakiyar tankar yaki ta siji [APC], sannan ya tabbatar da cewa za a tura jami’an tsaro na musamman don kwantar da hankalin al’umma.
A halin yanzu, rahotanni na cewa an samu kwanciyar hankali a yankin, amma ana ci gaba da sanya ido kan yanayin tsaro.