Ministan Harkokin Jinƙai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya zama sabon Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC a hukumance.

Yilwatda ya samu amincewar ne a ranar Alhamis, yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (National Executive Committee – NEC) na jam’iyyar da aka gudanar.
Bayan nadin nasa, yanzu ya shine zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus a watan da ya gabata, yana mai bayyana matsalolin lafiya a matsayin dalilin saukarsa.
Bayan saukar Ganduje, Ali Bukar Dalori, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Arewa, ya karɓi ragamar shugabanci a matsayin mukaddashi.
A baya dai, ana sa ran kwamitin NEC zai amince da Dalori ya ci gaba da rikon shugabancin jam’iyyar har zuwa lokacin gudanar da babban taron ta na Kasa inda za a zaɓi shugaba na dindindin, sai dai hakan bai faru ba, bayan da aka zaɓi tare da amincewa da Yilwatda kai tsaye.
Za a ci gaba da sa ido kan yadda sabon shugaban zai tafiyar da harkokin jam’iyyar a daidai lokacin da take shirin fuskantar kalubale da dama a fagen siyasar ƙasa.