Wata kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare, a jihar Kano, ta yanke wa wani matukin adaidaita sahu, Mansir Lawan, hukuncin daurin shekara guda da wata uku, bisa samunsa da laifin cin amana da kuma zanba.

Mansir, wanda mazaunin unguwar Gaida ne a yankin Yankusa, na fuskanci tuhuma ne bayan wani da ake kira Alasan Ahmed ya shigar da ƙara a ofishin ‘yan sanda ranar 21 ga watan Yuli.
A cewar karar, Alasan ya ba shi adaidaita sahu bisa tsarin haya purchase da kulla yarjejeniyar cewa zai biyan ₦850,000 a hakali a hankali. Idan ya kammala biya, mashin ɗin zai koma nasa. Sai dai, Mansir ya biya ₦480,000 kacal, daga bisani ya siyar da mashin ɗin ba tare da izini ba, kuma ya ɓace.
Lauyan gwamnati, Musabahu Usman, ya gabatar da ƙunshin tuhuma a gaban kotu, inda ya nemi a yanke hukunci nan take.
Mai shari’a Munzali Idris Gwadabe ya samu Mansir da laifin cin amana da zanba, inda ya yanke masa hukuncin daurin shekara guda ko tara ta ₦30,000 kan cin amana, da kuma wata uku ko tara ta ₦10,000 kan laifin zanba. Haka kuma, an umarce shi da ya biya ₦370,000 a matsayin kuɗin ranko ga mai ƙara.